<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 ) Yesu, ko tunawa da kai abu mai daɗi ne,
 Amma dai, daɗin ganinka, ina misalinsa?

[V2]
 2) Ba waƙar duniyan nan, ko ɗaya, ko zancen masana,
 Da za su iya kwatanta jamalin sunanka.

[V3]
 3) Mai tuba duk, sai begenka da gaskiya ya ke yi.
 Wanda ya nemi fuskarka, alheri nasa ne.

[V4]
 4) Amma fa masu samunka, ƙaunar da ka ke yi,
 Ba za a ga cikarta ba, sai wurin Masu Bi.

[V5]
 5) Ya Yesu, kai ne murnarmu a cikin duniyan nan,
 Kai za ka zama ladanmu a cikin Sama can.</lyrics>
<title>Yesu, Ko Tunawa Da Kai Abu Mai Daɗi Ne LW229</title>
<hymn_number>229</hymn_number>
</song>